Mphela na hannu saboda tuki cikin maye

Image caption Katlego Mphela

Dan wasan Afrika ta kudu Katlego Mphela na hannun jami'an tsaro a birnin Johannesburg, bayan an same shi da laifin tuki cikin maye.

An dai kama dan wasan ne ranar litinin kasa da sa'o'i 48 bayan da ya zura kwallon da ta ba kasarshi nasara akan Afrika ta kudu a wasan share fage na taka leda a gasar cin kofin kasashen Afrika.

"Gaskiya bai ji dadin abun da ya faru ba, saboda bai san yana cikin maye ba, da kuma ya san da haka da bai yi tuki ba", In ji Agent din Mphela.