Gerrard na shirin komawa fagen tamaula

gerrard
Image caption Steven Gerrard

Kaptin din Liverpool Steven Gerrard yace yana saran zai murmure don buga wasa tsakaninsu da West Brom a ranar Asabar bayan ya shafe kusan wata guda yana jinya.

Gerrard bai buga wasanni uku ba sakamakon tiyatar da aka yi mashi bayan wasan da Manchester United ta doke su daci uku da daya a ranar uku ga watan Maris.

Yace"Ina saran zan koma horo gadan-gadan a ranar Alhamis, kuma ya ragewa kocinmu, ko ya zabeni ko kuma a'a.

A halin yanzu Liverpool ce ta shida akan teburin gasar premier, inda take bayan Tottenham da maki hudu.

Gerrard ya kara da cewar ya zaku Andy Carroll da Luis Suarez su hadu su fara fasa ragar abokan hammaya.