Wasan AC Milan da Inter shine mafi mahimmanci-Allegri

allegri
Image caption Massimiliano Allegri

Kocin AC Milan Massimiliano Allegri ya ce wasa tsakaninsu da Inter Milan na ranar Asabar shine mafi mahimanci a tarihin horadda 'yan kwallo da yake yi.

Ganin cewar Tottenham ta fidda AC Milan daga gasar zakarun Turai, a halin yanzu Allegri na fuskantar matsin lamba don tabbatar da cewa makwabtansu basu kawo musu cikas ba.

Milan ta shiga gaban Inter da maki biyu akan teburin gasar Serie A a yayinda ya rage karawa takwas a kammala gasar ta Italiya.

Milan zata buga wasanne ba tare da Zlatan Ibrahimovic ba saboda dakatar da shi na wasanni biyu sakamakon laifin da yayi a wasansu da Bari.

Amma Allegri nada kwarin gwiwa akan Pato da Robinho da kuma Cassano zasu taimakawa tawagar don samun nasara.

A bangaren Inter kuwa Samuel Eto'o shine jigo wajen zira kwallo.