Manchester United na zawarcin golan Athletico Madrid

David De Gea Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption David De Gea

Manchester United ta fara tattaunawa akan batun sayen mai tsaron gidan Atletico Madrid David De Gea.

Wakilin dan kwallon Hector Rincon wanda ya tabbatar da hakan, ya ce manyan kulob kulob na Turai na zawarcin De Gea.

Dan wasan mai shekaru ashirin da haihuwa, a kwanannan an alkantashi da komawa Old Trafford don maye gurbin Edwin van der Sar wanda zai yi ritaya a karshen kakar wasan bana.

Ricon ya kara da cewar"a halin yanzu kwangilar De Gea bata kare ba a Athletico Madrid, amma za a iya sasantawa da duk kungiyar data nuna sha'awa akanshi".

Har wa yau rahotanni na nuna cewar Manchester United na zawarcin golan Schalke Manuel Neuer.