King na Tottenham zai yi jinya mai tsawo

king
Image caption Ledley King

Kaptin din Tottenham Ledley King akwai alamun ba zai kara taka leda ba a kakar wasa ta bana saboda rauni mai tsanani.

Kocin Spurs Harry Redknapp ya bayyana cewar dan kwallon bayan na bukatar tiyata a karo na biyu bayan ya dade yana jinya tun watan Oktoba.

Wannan raunin na Kings yazo a dai dai lokacin da Tottenham ke shirye shiryen fuskantar Real Madrid a zagayen gabda na kusada karshe a gasar zakarun Turai a ranar Talata mai zuwa.

A halin yanzu akwai shakku akan cewar William Gallas zai buga wasan na filin Bernabeu saboda rauni a gwiwarshi, sannan kuma Younes Kaboul da Jonathan Woodgate duk suna fama da rauni.

Amma dai Redknapp nada lafiyayyun 'yan kwallon baya guda biyu wato Micheal Dawson da Sebastian Bassong.