Hukumar EFA na goyon bayan Shehata a Masar

shehata
Bayanan hoto,

Hassan Shehata

Hukumar dake kula da kwallon Masar-EFA ta kawo karshen cece-kucen da ake yi akan makomar kocin 'yan kwallon kasar Hassan Shehata.

A halin yanzu Pharaohs din ce ta karshe akan teburin da take na neman gurbin zuwa gasar cin kofin kasashen Afrika, bayan ta sha kashi a wajen Afrika ta Kudu daci daya me ban haushi a ranar Asabar.

Saboda Masar din na tangal tangal, mutane suna kira a sallami Shehata duk da cewar ya jagoranci kasar ta lashe gasar cin kofin Afrika sau uku wato shekara ta 2006 da 2008 da kuma 2010.

Sanarwar da EFA ta fitar ta ce"bamu da tantama akan Hassan Shehara a matsayin kocin tawagar 'yan kwallonmu".

Shugaban EFA Samir Zaher ne ya kira taron gaggawa don tattaunawa akan makomar kasar a kokarin samun gurbin zuwa gasar cin kofin kasashen Afrika a 2012.