Manchester City ta lallasa Sunderland daci biyar

sunderland Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Adams Johnson ne ya fara cin kwallo

Manchester City ta shiga gaban Chelsea akan teburin gasar Premier inda City din ta lallasa Sunderland daci biyar da nema.

Adam Johnson dinne yaci kwallon farko sai Carlos Tevez yaci na biyu a fenariti a yayinda David Silva yaci na uku.

Patrick Vieira ne yaci kwallo na hudu sai kuma Yaya Toure yaci kwallo na biyar.

Wannan nasarar ta sa Manchester City na da maki hamsin da shida daga wasanni talatin da daya.

A daya wasan da aka buga ranar Lahadi, Fulham ta lallasa Blackpool daci uku da nema.

Bobby Zamora ne yaci kwallaye biyu sai Dickson Etuhu yaci kwallo daya.