An kawo karshen bajintar Mourinho a gida

mourinho Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jose Mourinho

An kawo karshen tarihin da Jose Mourinho ya kafa a matsayin koci inda ya shafe shekaru tara ba tare da an samu galaba akan kulob din da yake yiwa jagoranci a gidanta ba, sakamakon kashin da Real Madrid ta sha a wajen Sporting Gijon daci daya me ban haushi a filin Bernabeu.

Miguel de las Cuevas ne ya ci kwallon a minti na 79 wanda ya zamo rashin nasara ta farko a wajen Mourinho a gida cikin wasanni 151.

Kocin dan kasar Portugal ya buga wasanni 23 ba tare an doke Real ba gidanta a kakar wasa ta bana, bayan jagorantar Inter Milan da Chelsea inda suma ba a doke su ba a gida.

Wasan farko da aka doke kungiyarshi a gidanta shine lokacin yana Porto inda Beira-Mar ta doke su daci uku da biyu a shekara ta 2002.

Wannan sakamakon ya kawowa Real cikas a kokarinta na kalubalantar Barca a takarar lashe gasar La Liga ta bana.

Mourinho ya ce"azihiri bamu fidda ran lashe gasar ba, amma a gaskiya tazarar maki takwas da kamar wuya".