Gasar kwallon Masar na cikin hadari - Khaled Mortagey

kungiyar  Al Ahly
Image caption Gasar Masar na daga cikin mafiya kayatarwa a Afrika

Wani babban jami'i a Hukumar gudanarwa ta Al Ahly, ya yi gargadin cewa harkar kwallon Masar na gab da mutuwa idan hukumomi suka soke gasar League ta kasar.

Gasar wacce aka dakatar a watan Janairu saboda rikicin siyasar kasar, an kuma sake dageta bayan da 'yan kallo suka tayar da hargitsi a birnin Alkahira ranar Asabar.

Hukumar Kula da Kwallon kafa ta Masar za ta gana domin tattaunawa kan ci gaba da gasar, inda yiwuwar sake dakatar da gasar ke haifar da zullumi.

"Yawancin kungiyoyin kwallo za su talauce idan aka soke gasar," kamar yadda Khaled Mortagey ya shaida wa BBC.

"Wannan mataki mara kan gado daga mutanen da ke da hankali ne idan suka soke gasar - ko suka sake dage ta.