Za a koma gasar kwallon Masar a karshen mako

masar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Magoya bayan Zamalek a cikin fili

Za a koma buga kwallo a gasar Masar a karshen wannan makon, sakamakon rahotannin cewar cigaba da dakatar da gasar zai durkusar da wasu kungiyoyin.

An kara dakatar da shirin fara gasar ne saboda tashin hankalin daya auku a Alkahira lokacin gasar cin kofin zakarun Afrika.

Bayan roko daga wajen manyan kungoyoyin kasar, sai hukumar dake kula da kwallon Masar EFA ta canza shawara.

A halin za a fara gasar a ranar 13 ga watan Afrilu kuma 'yan kallo zasu hallarta.

A baya ana dakatar da gasar ce saboda yamutsin siyasa daya auku a kasar abinda ya kawo karshen mulkin Shugaban Hosni Mubarak.

Hukumar EFA ta ce Firayi Ministan kasar Esam Sharaf ya amince da batun.