Ba ma fuskantar matsin lamba-Redknapp

bale
Image caption Cristiano Ronaldo da Gareth Bale

Kocin Tottenham Harry Redknapp ya ce kulob dinshi baya cikin matsin lamba a yayinda suke shirin fuskantar Real Madrid a bugun farko na gasar zakarun Turai.

Spurs ta tafi Madrid don karawa da kungiyar data lashe gasar sau tara.

Redknapp yace"bana fuskantar matsin lamba, saboda babu wanda ya saran zamu kai wannan matakin a farko kakar wasa ta bana".

Kawo yanzu dai Tottenham ta taka rawar a gasar, inda ta fito a matsayin ta farko a rukunin da take wanda ya kunshi Inter Milan da Werder Bremen da kuma FC Twente, sannan kuma ta fidda AC Milan a wasan zagaye na biyu.

Spurs dai ta buga wasanni uku a jere tana tashi babu ci abinda kuma take bukatar ta gyara kafin fuskantar matasan Jose Mourinho.

Sai dai itama Real a ranar Asabar ta sha mamaki inda Sporting Gijon ta doke ta gida.