Dan wasan Newcastle Best zai yi jinya mai tsawo

Leon Best
Image caption Leon Best

Dan kwallon Newcastle United Leon Best ba zai kara taka leda ba a kakar wasa ta bana saboda rauni a gwiwar.

Best mai shekaru da hudu za ayi mashi tiyata a karo na biyu a kakar wasa ta bana.

Best yaci kwallaye shida cikin wasanni goma da aka fara dashi a Newcastle a kakar wasa ta bana.

Bayan tafiyar Andy Caroll, Best ya samu dama don jan ragamar 'yan kwallon gaba a Newcastle.

Kuma ya zira kwallaye uku a wasansu da West Ham sai kuma kwallaye biyu a wasansu da Arsenal da kuma Birmingham.

Wannan raunin da Best ya samu ya janyo Magpies nada 'yan wasan gaba uku kadai suka rage Shefki Kuqi da Nile Ranger da kuma Shola Ameobi.