Schalke ta lallasa Inter Milan

Schalke ta lallasa Inter Milan
Image caption Wannan wasa dai ya ba masu sharhi mamaki matuka

Schalke 04 ta zira kwallaye uku bayan hutun rabin lokaci, inda ta lallasa mai rike da kanbun zakarun Turai Inter Milan da ci 5-2 a wasan dab da na kusa da na karshe.

Wasan wanda aka buga a filin wasa na San Siro dake Italiya, an baiwa dan wasan Inter na baya Cristian Chivu jan kati, abinda ya tarwatsa bayan Inter.

An tafi hutun rabin lokaci ne dai kungiyoyin na da ci biyu da biyu.

Amma bayan an dawo sai Schalke 04 ta ci gaba da ruwan kwallaye, inda ta zira uku ciki kuwa harda daya ta Raul Gonzales.

Kocin Inter Milan dai Leonardo, ya ce zai yi wuya Inter ta kai labari ganin yadda aka yi mata ruwan kwallaye.