Jan kati ne ya dakile mu - Redknapp

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tottenham ta shafe mintina 75 tana wasan da mutane 10

Kocin Tottenham Harry Redknapp ya ce jan katin da aka baiwa Peter Crouch ne ya hanasu katabus a wasan da Real Madrid ta lallasa su da ci 4-0.

Alkalin wasa ya kori Peter Crouch ana minti na 14 da fara wasan, bayan da ya samu katin gargadi guda biyu a wasan dab da na kusa da na karshe na gasar zakarun Turai.

"Abu ne mai matukar wahala mu kai labari da mutum 10," a cewar Redknapp. "Kana bukatar mutane 11 domin taka rawa a irin wannan wasan.

"Har yanzu wasan bai kare ba, amma kalubalen dake gabanmu yana kama da daukar dala ba ganmo."

Tsohon dan wasan Arsenal Adebayor ne ya zira kwallon farko biyu yayin da Angel di Maria da Cristiano Ronaldo suka zira dai-dai.