Boateng na Jamus zai yi jinya ta makwanni shida

boateng Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Jeroma Boateng

Dan kwallon Manchester City Jerome Boateng zai shafe akalla makwanni shida yana jinya bayan tiyatar da aka yimashi a gwiwa.

Dan shekaru ashirin da biyu, an yi mashi tiyatar ne a Jamus bayan ya jimu a gwiwarshi ta dama a wasan Jamus da Kazakhstan.

Boateng wanda ya bugawa Jamus a wasanni 13, a halin yanzu rahotanni na cewar Bayern Munich na zawarcinshi.

Kocin City Roberto Mancini ya ce Boateng akwai alamun ba zai kara taka leda a kakar wasa ta bana.