Ribery da Gomez na nan daram a Bayern Munich

ribery
Image caption Franck Ribery

'Yan kwallon Bayern Munich Mario Gomez da Franck Ribery sun sha alwashin cigaba da kasance a kulob din.

Sun kuma nuna goyon bayansu akan shugaban kungiyar Uli Hoeness.

Ribery dan Faransa kwangilarshi zata kare ne a shekara ta 2015 a yayinda kwangilar Gomez zata kare a shekara ta 2013.

Ribery ya shaidawa wata jarida cewar"zan cigaba da kasancewa a Bayern saboda ina jin dadi".

Gomez kuwa wanda ya zira kwallaye 30 a wasanni daban daban tare da Bayern ya ce yana nan daram a kulob din.

Shi kuwa dan kwallon Holland Arjen Robben ya tabbatar da cewa zai bar kulob din saboda bai shirya buga gasar Europa ba.

A halin yanzu Bayern Munich ce ta uku akan teburin gasar Bundesliga, kuma tana bukatar kasancewa ta biyu ne don samun gurbin zuwa gasar zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa.