An dakatar da Rooney na tsawon wasanni biyu

Image caption Wayne Rooney

Wayne Rooney ba zai taka leda ba a wasan kusa dana karshe da Kungiyarshi ta United za ta fafata da City a gasar cin kofin FA.

Hukumar FA ta Ingila dai ta jaddada dakatarwar da tayiwa Ronney duk da daukaka karar da ya yi na neman ahuwa.

An dakatar da dan wasan ne bayan ya yi wasu kalamai a gaban na'uran daukan hoton talbijin a filin wasan na Upton Park bayan da ya zura kwallo a wasan da United ta doke West Ham.

Rooney dai ya amsa laifin da ya yi amma ya nemi ahuwa, inda ya ce matakin da hukumar FA ta dauka ya yi tsanani.

Dan wasan ba zai samu taka leda ba a wasan da kungiyar za ta kara da Fulham a gasar Premier a ranar asabar.