Za a koma gasar kwallon Tunisia a wannan watan

tunisia Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An shafe watanni uku ba a kwallo a Tunisia

Za a koma buga gasar kwallon Tunisia a ranar 17 ga watan Afrilu bayan tsaiko na watanni uku.

An dakatar da gasar ce a watan Junairu sakamakon tashin hankalin siyasar daya kawar da shugaba Zine al-Abidine Ben Ali.

A watan daya gabata an yi kokari maidoda da gasar amma sai akan dakatar saboda fargaba ta tsaro.

Amma a yanzu mahukunta kwallon kafa da jami'an tsaro sun amince a koma gasar kuma 'yan kallo zasu iya shiga kallo.

An buga wasanni biyu na gasar zakarun Afrika a Tunisia tun bayan juyin juya hali, amma ba a buga gasar cikin gida a yayinda ake tunanin cigaba da dakatar zai yi durkusar da kulob kulob na kasar.