Man U za ta kara da Juve don girmama Gary Neville

Gary Neville
Image caption Gary Neville na daga cikin tsofaffin 'yan wasan United

Manchester United za ta kara da Juventus a wani wasan sada zumunta da aka shirya domin girmama Gary Neville a filin wasa na Old Trafford a ranar 24 ga watan Mayu.

Neville, mai shekaru 36, ya sanar da ritayarsa ne a ranar 2 ga watan Fabreru bayan ya shafe rayuwar kwallonsa a United, inda ya buga wasanni 602.

Ya ce: "Na ji dadi ganin yadda aka shirya wannan wasan saboda ni, wasan zai zamo mai karsashi, musamman ganin yadda zan cire jan rigar United.

"Ina shirin nuna farin ciki na a ranar, kuma ina fatan magoya baya za su taya ni," kamar yadda ya kara nana tawa.

Neville ya fara taka leda a United ne tun yana dan shekaru 17 a wasan da suka kara da Torpedo Moscow a gasar cin kofin Uefa a shekarar 1992.