La Liga:Barcelona da Real Madrid sun haskaka

messi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Lionel Messi

Barcelona wacce ke kokarin kare kofin data lashe a bara, ta kara daure damara inda ta lallasa Almeria daci uku da daya.

Lionel Messi ne ya zira kwallaye biyu sai kuma Thiago yaci daya a yayinda Corona ya ciwa Almeria kwallo daya.

Itama Real Madrid wacce ke yiwa Barca matsin lamba ta samu galaba akan Athlectic Bilbao daci uku da nema.

Kaka ya zira kwallaye biyu sai Christiano Ronaldo wanda yaci kwallo daya.

A yayinda ya rage wasanni bakwai a gasar ta La Liga, Barcelona nada maki tamanin da takwas sai kuma Real Madrid mai maki saba'in da shida.