United zata iya lashe kofina uku a bana-Hughes

ferguson Hakkin mallakar hoto
Image caption Alex Ferguson

Kocin Fulham Mark Hughes ya ce Manchester United zata lashe kofina uku a kakar wasa ta bana, bayanda kungiyarshi ta sha kashi a wajen United.

A halin yanzu United ce ke jan ragamar gasar Premier kuma ta samu galaba akan Chelsea a bugun farko na gasar zakarun zakarun Turai a yayinda take jiran buga wasan zagayen kusada karshe a gasar cin kofin FA.

Hughes yace"zasu iya lashe komai".

United ta lashe kofina uku a shekarar 1999 inda ta doke Bayern Munich a wasan karshe na gasar zakarun Turai, sai kuma ta casa Newcastle a wasan karshe na kofin FA Cup sai kuma ta lashe gasar premier.

Red Devils din dai sun lallasa Fulham ne daci biyu da nema inda Dimitar Berbatov da Antonio Valencia suka zira kwallayen.