Bougherra ya ki amincewa da sabunta kwangilarshi a Rangers

Madjid Bougherra Hakkin mallakar hoto b
Image caption Madjid Bougherra

Dan kwallon Rangers Madjid Bougherra ya ki amincewa da tayin sabunta kwangilarshi na karin shekaru biyu masu zuwa.

Dan wasan na Algeriya wanda ya koma Rangers daga Charlton a shekara ta 2008 nada sauran shekara guda kafin kwangilarshi ta kare a Scotland amma ya ce yafi ya koma Ingila.

Bougherra yace "Rangers ta bani damar sabunta kwangila ta amma nace a a, tunda na shafe shekaru uku anan, ina bukatar kalubale na daban".

A halin yanzu Bougherra ya samu rauni a lokacin wasansu da Celtis a watan daya gabata.

Ya kara da cewar"a yanzu abinda nakeso shine komawa gasar premier, amma idan bai yiwuba zan koma ko Turkiya ko kasashen Larabawa".