Ina son zira kwallaye 15 a kakar wasa ta bana-Odemwingie

Peter Odemwingie
Image caption Peter Odemwingie

Dan kwallon West Bromwich Peter Odemwingie ya sa kanshi burin zira kwallaye goma sha biyar a kakar wasa ta bana.

A halin yanzu dan Najeriya din ya ci kwallaye goma sha daya a kakar wasa ta bana hadda kwallon daya zira a wasansu da Sunderland.

Yana bukatar karin kwallaye hudu don wuce 14 da ya zira a kungiyar Lille ta Faransa a kakar wasa ta 2005-06.

Odemwingie yace"burina shine in wuce kwallaye sha hudu, tunda akwai sauran wasanni shida kafin a kammala gasar, tabbas hakan na yiwuwa".

Albion a halin yanzu itace ta goma akan teburin gasar premier kama ba'a samu galaba akanta ba tunda akan nada Roy Hodgson a matsayin koci.