An dakatar Arjen Robben na wasanni biyu

robben
Image caption Arjen Robben

An dakatar da dan kwallon Bayern Munich Arjen Robben na wasanni biyu masu zuwa.

Wannan haramcin ya nuna cewar dan wasan ba zai buga wasansu da Bayer Leverkusen ba, wanda zai bayyana ko Bayern zata samu gurbin zuwa gasar cin kofin zakarun Turai ko kuma a a.

An kori Robben ne bayan ya zagi alkalin wasa lokacin da aka kamala karawa tsakanin Bayern da Nuremberg inda aka tashi kunen doki.

Hukumar kwallon Jamus ce ta dakatar da Robben din.

Bayan wasan ne kuma aka kori kocin Bayern din Louis van Gaal, a yayinda mataimakinshi Andries Jonker zai jagoranci Bayern a wasanni biyar da suka rage a kakar wasa ta bana.