Zan kawo Ronaldo AC Milan, idan muka lashe gasa

cristiano
Image caption Cristiano Ronaldo

Mai kungiyar AC Milan Silvio Berlusconi ya bayyana aniyar sayen dan kwallon Real Madrid Cristiano Ronaldo idan har kungiyarshi ta lashe gasar Serie A.

A yayinda ya rage wasanni shida a kamalla gasar, Milan ce ke jagoranci inda ta dara Napoli da maki uku sannan tafi Inter da maki biyar.

Firayi Ministan Italiyan ya bayyana sha'awarshi na kulla yarjejeniya da tsohon dan kwallon Manchester United mai shekaru ashirin da shida, duk da cewar Ronaldo din bai ce yanason ya bar Santiago Bernabeu.

Berlusconi yace"idan muka lashe gasar Serie A, to da zarar an bude kasuwar musayar 'yan kwallo, zamu sayi sabbin 'yan wasa hadda Ronaldo".

Ya kara da cewar "idan har na kara Ronaldo cikin tawaga ta, ina tunanin barina ya cika".

Idan har AC Milan ta lashe gasar, shine zai zamo a karon farko tun shekara ta 2004.

Har wa yau tawagar AC Milan ta yanzu na cike da tsaffin 'yan wasa kamarsu Clarence Seedorf da Andrea Pirlo.