John Mensah zai yi jinya ta makwanni uku

mensah
Image caption John Mensah

Dan kwallon Sunderland John Mensah zai shafe watanni uku yana jinya bayan ya jimu lokacin karawarsu da West Brom.

Dan wasan Ghana, mai shekaru ashirin da takwas, wannan jinyar ta nuna cewar ba zai taka leda a watan Afrilu.

Hakan na nufin cewar ba zai buga wasansu da Birmingham da Wigan da kuma Fulham.

Mensah ya dade yana fama da rauni a kakar wasanni biyu da suke wuce.

A halin yanzu Sunderland na fama da karancin 'yan kwallo saboda rauni irinsu Kieran Richardson da Anton Ferdinand.

Sunderland dai itace ta goma sha uku akan teburin gasar premier inda take da maki 38 cikin karawa 32.