Olympics 2012:Najeriya zata kara da Tanzania

olympics
Image caption Najeriya ce ta lashe gasar kwallon Olympics a 1996

Sudan wacce ta fidda Ghana a wasan neman gurbin zuwa gasar kwallon maza na Olympics a 2012 zata kara da Masar a wasan zagaye na biyu.

Tanzania wacce ta fidda Kamaru zata hadu da Najeriya wacce ta lashe gasar a shekarar 1996.

Duk kasar data samu nasara a karawa tsakanin Liberia da Ivory Coast zata fafata da Congo Brazzaville.

Kasashen Afrika uku zasu tsallake zuwa gasar Olympics ta badi a London, a yayinda kasa ta hudu zata buga wasan kifa daya kwala tsakaninta da wata kasa a yankin nahiyar Asiya.

Za ayi bugun farko na wasannin zagaye na biyu ne a karshen makon 3-5 ga watan Yuni sai kuma a juya bayan makwanni biyu.

Yadda aka rarraba kasashen a zagaye na biyu:

Tanzania v Najeriya

Algeria v Zambia

Morocco v DR Congo

Congo v Ivory Coast ko Liberia

Gabon v Mali

Sudan v Masar

Benin v Afrika ta Kudu

Tunisia v Senegal