McCarthy na Afrika ta Kudu ya bar West Ham

Dan kwallon Afrika ta Kudu Benni McCarthy ya fice daga West Ham bayan ya katse kwangilarshi da kulob din.

Dan wasan mai shekaru talatin da uku, ya kasa tabuka abun a yazo a gani a Upton Park, inda ya kasa cin kwallo a wasanni 14 da ya buga tun zuwanshi daga Blackburn Rovers a watan Fabarairu na shekara ta 2010.

Sanarwar da kulob din ta fitar ta ce"West Ham ta amince na barin Benni McCarthy ba tare da bata lokaci ba".

Ta kara da cewar"kulob din na yiwa Benni fatar alheri".

McCarthy ya buga wasanni biyu ne kacal a gasar premier tun zuwanshi West Ham wattani 14 da suka wuce.

Tsohon dan kwallon Porto din ba a sakashi cikin tawagar 'yan kwallon West Ham ashirin da biyar saboda zuwan Robbie Keane da Demba Ba.