Amos Adamu zai iya daukaka kara zuwa CAS

Amos
Image caption Amos Adamu ya rasa kujerarshi a FIFA

Babban jami'in kwallon kafa a Najeriya Amos Adamu nada damar daukaka kara zuwa kotun sauraron kararrakin wasanni wato CAS akan batun dakatarwar da FIFA tayi mashi na shekaru uku.

Kafofin yada labarai sunyi zargin cewar lokaci ya kurewa Amos na daukaka karar, tun da Fifa ta tabbatar da dakatarwar a ranar 7 ga watan Fabarairu.

Amma Fifa ta shaidawa BBC cewar sai a ranar 12 ga watan Afrilu aka bata a rubuce yadda lamarin yake.

Adamu wanda aka dakatar bisa zargin karbar cin hanci wajen zaben kasashen da zasu dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a 2018 da 2022, nada damar daukaka kara daga nan zuwa uku ga watan Mayu.

Dokar Fifa ta tanadar cewa duk wanda yake son ya daukaka kara sai ya bada a rubuce cikin kwanaki 21 da daukar hukuncin.

Mutumin da zai daukaka karar nada karin wasu kwanaki goma don aikewa FIFA da kotun sauraron kararakin wasanni wato CAS duka takardun da suka dace.

Image caption Amos Adamu da Reynald Temari sune aka zarga

Kafin a dakatar da Adamu, ya kasance wakili a kwamitin gudanarwar Fifa dana hukumar kwallon Afrika wato CAF sannan kuma shine shugaban hukumar kwallon yammacin Afrika wato WAFU.

A watan Fabarairu, Adamu ya shaidawa BBC cewar zai daukaka kara zuwa CAS, wato babbar hukumar da ke warware matsalolin da suka shafi wasanni, amma har yanzu bai kara tabbatarwa ba cewar zai cigaba da kalubalantar matakin.