London 2012: Sudan za ta kara da Masar

London 2012 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kasashen Afrika sun sha taka rawar gani a gasar Olympics

Sudan za ta kara da kasar Masar a wasan share fage na shiga gasar kwallon kafa ta Olympics da za a yi a London a shekara ta 2012.

Tanzania, wacce ta doke Kamaru za ta fafata ne da Najeriya, wacce ta taba lashe gasar a shekarar 1996.

Haka kuma duk wanda ya samu nasara a karawa tsakanin Liberia da Ivory Coast, zai hadu ne da Congo Brazzaville.

Za a buga wasan ne a birnin Monrovia a ranar 20 ga watan Afrilu, inda Ivory Coast ke jagoranci da ci 4-0.

Duka kungiyoyi takwas da suka samu nasara za su tsallake zuwa zagayen karshe, wanda kuma ba a son tsarin da za a bi ba.

Kasashe uku ne dai za su tsallake kai tsaye, yayin da cikon na hudun zai buga wasan kifa daya kwala da kasar Asia.

Za a buga karon farko na wasannin ne a ranakun 3-5 ga watan Juni da zagaye na biyu makwanni biyu baya.

Yadda wasannin za su kasance

Algeria da Zambia

Morocco da DR Congo

Congo da Ivory Coast ko Liberia

Gabon da Mali

Sudan da Egypt

Benin da South Africa

Tunisia da Senegal

Tanzania da Nigeria