Arsenal ta gamu da cikas a filin Emirates

wengetr
Image caption Arsene Wenger

Yin kurin Arsenal na lashe gasar premier a bana ya kara fuskantar koma baya sakamakon buga kunen doki tsakaninta da Liverpool a filin Emirates.

Gunners din sun dauka sun samu nasara a wasan lokacin da Robin van Persie yaci fenariti a minti na 98 sakamakon kada Cesc Fabregas da Jay Spearing yayi.

Amma kuma bayan mintuna hudu sai Emmanuel Eboue ya kada Lucas Leiva abinda ya baiwa Dirk Kuyt damar farkewa Liverpool kwallon.

A halin yanzu Manchester United ta dara Arsenal da maki shida a yayinda ya rage wasanni shida a kamalla gasar.

Sakamakon wannan wasan dai ya janyowa Arsene Wenger murna ta koma ciki saboda tazarar da United ta bashi.