AYC: Mali ta doke Afrika ta Kudu

ayc
Image caption Gasar matasan Afrika

Mali ta fara gasar cin kofin matasan Afrika da kafar dama inda ta doke Afrika ta Kudu daci hudu da biyu a wasan farko na gasar.

Abdoulaye Coulibaly ya ciwa Mali kwallaye biyu a wasan da aka buga a Johannesburg.

Cheick Mohamed Cherif Doumbia da Ibrahim Diallo shima ya ciwa Mali kwallo a yayinda Amajita da Lucky Nguzana suka ciwa Afrika ta Kudu kwallayenta.

Mali zata kara da Masar a wasanta na gaba a ranar Laraba a yayinda ita kuma Afrika ta Kudu zata hadu da Lesotho.

Kasashe hudu daga cikin takwas din da ke fafatawa a gasar ne zasu wakilci Afrika a gasar kofin duniya a Colombia a watan Yuli.