Man United za ta farfado - Van der Sar

Edwin van der Sar
Image caption Edwin van der Sar yana taka rawa sosai a Man United

Mai tsaron gidan Manchester United Edwin van der Sar, ya ce kungiyar ba za ta fuskanci matsala ba a wasan da za ta kara da Newcastle a gasar Premier a ranar Talata.

A ranar Asabar ne dai Mancheaster City ta fitar da Man United daga gasar cin kofin FA.

Amma kunnen dokin da Arsenal ta yi da Liverpool ranar Lahadi, ya nuna cewa maki shida ne tsakanin United da Arsenal - kuma saura wasanni shida a kammala gasar.

"Abu ne mai wahala mu yi sakaci. Mun san mahimmancin gasar League," a cewar Van der Sar.

"Mu ne a kan gaba, don haka wajibi ne mu yi iya yin mu domin kaiwa ga gaci.