Tottenham zata yi ran gadi a Afrika ta Kudu

redknapp
Image caption Harry Redknapp

Tottenham za ta kai ran gadi zuwa Afrika ta Kudu a watan Yuli.

A lokacin rangadin, Spurs din zata kara da Kaizer Chiefs da kuma kungiyar Orlando Pirates.

Kungiyar ta Tottenham a ranar 16 ga watan Yuli zata kara da Chiefs sannan bayan kwanaki uku ta fafata da Pirates.

Daga bisani kuma Spurs din zata hadu da duk kungiyar data samu nasara a tsakanin Chiefs da Pirates a ranar 23 ga watan Yuli.

A shekara ta 2007, 'yan Spurs din sun ziyarci Afrika ta Kudu.