Kofin FA: Stoke ta lallasa Bolton da ci 5-0

Robert Huth
Image caption Robert Huth na daga cikin wadanda suka zira kwallayen

Kwallaye uku da aka zira a zagayen farko sun baiwa Stoke City damar lallasa Bolton Wanderers da ci 5-0, inda suka kai ga wasan karshe na gasar cin kofin FA a karon farko a tarihinsu.

Matthew Etherington da Robert Huth da Kenwyne Jones ne suka zira kwallayen a mintina talatin na farko.

Bayan an dawo hutun rabin lokaci ne kuma Jon Walters ya zira kwallaye biyu a wasan da aka fafata a filin wasa na Wembley.

A yanzu Stock City za ta kara ne da Manchester City a wasan karshe, bayan da City ta doke Manchester United da ci daya mai ban haushi.

Za dai a buga wasan karshen ne a filin wasa na Wembley a ranar 14 ga watan Mayu.