Barcelona na kalubalantar dakatarda Iniesta

iniesta Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Andres Iniesta

Barcelona na kalubalantar matakin hukumar kwallon kafa ta Turai wato UEFA na kokarin dakatar da Andres Iniesta daga buga wasanta da Real Madrid a bugun farko na zagayen kusada karshe a gasar zakarun Turai.

A halin yanzu ana binciken Iniesta bayan da aka bashi katin gargadi a wasa tsakaninsu da Shakhtar Donetsk wanda ke nuna cewar watakila ba zai buga wasan zagayen kusada karshe ba.

Barca tace "manufa ta alheri na dan wasan, zai taimaka mana wajen hana dakatar dashi".

Shi kuwa kocin Real Madrid Jose Mourinho da kuma Xabi Alonso da Sergio Ramos duk an tabbatar da cewar sun aikata ba dai dai ba.

'Yan wasan biyu duk an kore su a wasan Real da Ajax a watan Nuwamban 2010 inda Real ta samu galaba daci hudu da nema.