'Yan Barcelona da Real Madrid sun fi karbar albashi

messi_ronaldo
Image caption Lionel Messi da Cristiano Ronaldo

Manyan kungiyoyin kwallon kafa a Spain wato Barcelona da Real Madrid suna biyan 'yan kwallonsu akalla dala miliyan bakwai a kowacce shekara.

Kungiyoyin biyu wadanda ke cikin manyan kungiyoyi uku na farko a duniya mafi arziki, sun shiga gaban kungiyar base ball ta New York Yankees, wacce a baya itace tafi biyan 'yan wasa a duniya.

Kididdigar da aka fitar ta nuna cewar akalla mafi karancin abinda ake baiwa dan wasa a Barcelona ya kai dala miliyan 7.9 sai kuma Real Madrid wacce ke bada dala miliyan 7.4.

Yankees din akalla ta biyan 'yan wasanta mafi karanci dala 6.8.

'Yan wasan da suka fi samun kudi a Ingila sune na Chelsea wacce take ta shida.

Kungiyoyin kwallon kwando na LA Lakers da kuma Orlando Magid sune na hudu da biyar.