AYC:Kamaru ta casa Najeriya daci daya

ayc
Image caption Kamaru ta jikawa Najeriya gari

Kamaru ta doke Najeriya daci daya me ban haushi a kokarinta na samun gurbin zuwa zagayen kusada karshe na gasar cin kofin matasan Afrika 'yan kasada shekaru ashirin da ake fafatawa a Afrika ta Kudu.

Franck Ohandza shine ya zira kwallon kafin a tafi hutun rabin lokaci a wasan da suka buga a Johannesburg.

Tawagar Baby Lions sun murza leda matuka a wasa, amma 'yan Flying Eagles sun barar da dama masu yawa.

Bayan wasanni biyu a yanzu Kamaru ce ke kan gaba a rukunin B da maki shida sai Najeriya mai maki uku.

Idan har Flying Eagles na son su kai zagayen kusada karshe to dole ne sai sun casa Gambia a ranar Lahadi.

A yayinda ita kuma Kamaru zata kece raini da Ghana a daya wasan na ranar Lahadi.ayc