Real Madrid ta doke Barcelona

Real Madrid ta doke Barcelona Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan ne karo na farko da Real ta doke Barca tun 2008

Kwallon da Cristiano Ronaldo ya zira a karin lokaci, ta baiwa Jose Mourinho damar lashe kofi na farko bayan zuwansa Real Madrid, inda suka doke Barca da ci 1-0 a wasan karshe na kofin Copa del Rey.

Bayan da aka shafe mintina 90 ana fafatawa babu wanda ya yi nasara, an tafi karin lokaci inda a zagaye na farko Ronaldo ya zira kwallonsa ta 42 a kakar bana.

Mai tsaron gidan Real Madrid Iker Casillas, ya taimakawa Real din sosai inda ya hana Lionel Messi da Andres Iniesta a karo da dama.

Di Maria ya samu katin gargadi na biyu ana gab da kammala wasan, amma duk da haka Real sun sha.

"Na yi murnar lashe kofin Copa del Rey - nasara ce ta musamman," a cewar kocin Real Jose Mourinho. "Nasara ce mai kayatarwa da muka samu a kan babbar kungiya kamar Barcelona - kuma mun cancanci samunta."

Ronaldo, wanda ya zira kwallo dayan da ta raba rigima a wasan, ya ce ya yi amanna cewa zira kwallo da farko na da mahimmanci a wasan.