Etoile ta katse ziyara zuwa Najeriya

Kungiyar kwallon kafa ta Etoile du Sahel ta katse ziyarar da za ta kawo Najeriya, domin fafatwa a gasar zakarun kungiyoyin Afrika saboda fargabar rashin tsaro a kasar.

Etoile dai ya kamata ta fafata da kungiyar Kaduna United ne a Kaduna a zagaye na uku na gasar a ranar lahadi.

Kaduna na daya daga cikin garuruwan da rikicin siyasa ta barke a Najeriya, inda jami'an tsaro su ka ce akalla mutane 32 sun rasa rayukansu.

Tarzoma ta barke ne a Najeriya bayan da aka bayyana shugaba Goodluck Jonathan a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.

Kungiyar Etoile ta ce za ta kai ziyarar kasar muddin ofisin jakadancin Tunisaia dake Najeriya ya bata tabbacin cewa akwai kyakyawar tsaro.

Hukumar kwallon Afrika wato Caf za ta dakatar da kungiyar na tsawon shekaru biyu muddin ta kauracewa wasan ba tare da izinin ta ba.