Mai yiwuwa Essien ya buga wasan Chelsea da Spurs

 Michael Essien
Image caption Michael Essien ya sha fama da rauni a baya

Mai yiwuwa dan wasan Chelsea Michael Essien ya warke domin fafatawa a wasan Chelsea da Tottenham a gasar Premier ta Ingila a ranar Asabar.

Dan wasan, mai shekaru 28, an cire shi ne a wasan da Chelsea ta lallasa West Ham da ci 3-0 bayan da ya samu rauni.

Kuma hakan ya sanya shakku inda aka yi zaton Essien ya samu mummunan rauni.

Amma Chelsea ta bayyana a ranar Talata cewa: "Tiyatar da aka yi masa ta nuna cewa babu wata matsala sosai."

"Za mu duba halin da yake ciki mu gani zuwa karshen mako domin ganin ko zai iya taka leda a wasan Spurs."