Muna sahun gaba-gaba a Premier - Hughes

Mark Hughes
Image caption Mark Hughes ya taka rawa sosai a Fulham

Kocin Fulham Mark Hughes ya nuna farin ciki kan nasarar da kungiyarshi ta Fulham ta samu da ci 3-0 a kan Bolton inda yanzu suka zamo a mataki na 9 a teburin Premier ta Ingila.

Clint Dempsey ne ya zira kwallaye biyu yayin da Brede Hangeland ya zira daya, abinda ya tabbatar da Fulham din a gasar Premier.

Hughes ya ce: "Ina ganin mun yi nasara sosai. Muna sahun kungiyoyi goman farko yanzu.

"Wannan ne karo na farko da muka samu kanmu a wannan matsayin, kuma ya rage na mu mu tabbatar mun kasance a wurin har zuwa karshen kakar bana". "Muna da 'yan wasa masu kyau, mun taka leda yadda ya kamata don haka ina ganin mun cancanci kasancewa a sahun kungiyoyi goma na farko," kamar yadda ya nanata.