Taiwo na fuskantar tuhumar rashin da'a

Image caption Taye Taiwo

Dan wasan Najeriya Taye Taiwo zai fuskanci kwamitin ladabtarwa na hukumar kwallon Faransa a ranar 5 ga watan Mayu domin amsa tuhumar kalamun da basu dace ba.

Idan dai an samu Taiwo da laifi, hukumar kwallon Faransa za ta dakatar da shi.

Har wa yau shima kwamitin ya nemi abokin taka ledarsa wato Stephane Mbia da ya bayyana a gabansa.

Ana dai zargin Taiwo da rera wata waka dake adawa da kungiyar Paris St Germain, wakar da kuma ke dauke da wasu kalamun batanci.

Taiwo ne dai ya zura kwallon da ya ba Marseille nasara inda ta doke Montpellier da ci daya mai ban haushi a filin wasa na Stade de France.

Bayan wasan ne dai Taiwo ya rera wakar da ake tuhumarsa da ita.

Tuni dai dan wasan ya nadama kuma a ranar lahadi ya nemi ahuwa game da rashin da'ar da ya nuna.