'Yan wasan Barcelona sun cika lakwalakwa- Adebayor

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Emmnuel Adebayor na takawa Madrid leda ne na wucin gadi daga Man City.

Dan wasan Real Madrid Emmanuel Adebayor ya soki 'yan wasan Barcelona dan yin lakwalakwa idan an dan taba su.

Dan wasan ya furta hakan ne bayan da kungiyarshi ta sha kashi a hannun Barcelona da ci biyu da nema a wasan kusa dana karshe a gasar zakarun Turai.

An sallami dan wasan Real Pepe a wasan bayan da ya tade Dani Alves ana minti 61 da wasan.

Amma Adebayor ya ce: "Akwai yiwuwar Pepe ya aikata fawul, amma bai kamata ace an sallame shi ba.

"Duk sanda wata kungiya ke taka leda da Barca, idan an taba su, sai kaga sun fadi a kasa suna kuka kamar 'yan kananan yara."

A duk wasanni da Real Madrid ta buga da Barcelona a kakar wasan bana, sai da aka sallami dan wasan Real.

"Barcelona na da kwararrun 'yan wasa, amma bai kamata suna irin wadannan dabi'u ba."