Borussia Dortmund ta lashe gasar Bundesliga

Borussia Dortmund
Image caption Borussia Dortmund

Borussia Dortmund ta lashe gasar Bundeliga ta Jamus a yayinda ya rage wasanni a kamalla taka leda a gasar.

Dortmund ta daga kofinne bayan ta casa Nuremberg daci biyu da nema a ranar Asabar.

Ita kuwa Bayer Leverkusen wacce ta biyu ta sha kashi ne a wajen FC Cologne daci biyu da nema.

Sakamakon ya nuna cewar Dortmund ta shi gaban Leverkusen da maki takwas.

Lucas Barrios da Robert Lewandowski ne suka ciwa Dortmund kwallayen, wanda shine kofin Bundesliga na bakwai da kungiyar ta lashe sannan kuma a karon farko tun shekara ta 2002.

Borussia a kakar wasa ta bana ta lashe wasanni 22 cikin 32 idan aka doke ta a guda hudu a yayinda ya rage wasanni hudu a kamalla gasar.

Sakamakon wasu karawar Bundesliga na karshen mako:

*Köln 2 - 0 Bayer Leverkusen *Hoffenheim 1 - 2 Stuttgart *Mainz 05 3 - 0 Eintracht Frankfurt *Hannover 96 0 - 1 Borussia M'gladbag *Hamburger SV 0 - 2 Freiburg *Bayern München 4 - 1 Schalke 04