Arsenal ta jikawa Manchester United gari

premier
Image caption Manchester United da Chelsea da Arsenal suna fadan karshe

Har yanzu babu kungiyar dake da tabbacin lashe gasar premier ta Ingila a bana sakamakon wasanda Arsenal ta samu galaba akan Manchester United daci daya me ban haushi.

Aaron Ramsey ne ya baiwa Arsenal nasarar a wasan da aka buga a filin Emirates, abinda ke nuna cewar da akwai sauran rina a kaba a kokarin United na lashe gasar premier a karo na goma sha tara.

Chelsea wacce ke ta biyu akan tebur bayan ta lallasa Tottenham daci biyu da nema, kuma wasan Chelsea da Manchester United da zasu buga a mako mai zuwa shine tamkar wanda zai nuna kungiyar da zata lashe gasar.

Sakamakon sauran karawar gasar premier:

*Liverpool 3 - 0 Newcastle United *Arsenal 1 - 0 Manchester United *Manchester City 2 - 1 West Ham United *Birmingham City 1 - 1 Wolverhampton *Blackburn Rovers 1 - 0 Bolton Wanderers *Blackpool 0 - 0 Stoke City *Sunderland 0 - 3 Fulham *West Bromwich … 2 - 1 Aston Villa *Wigan Athletic 1 - 1 Everton *Chelsea 2 - 1 Tottenham Hotspur