Siasia na lallabar Sidney ya bugawa Najeriya

sidney sam Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sidney sam

Samson Siasia na kokarin shawo kan matashin dan kwallon Jamus Sidney Sam ya koma bugawa Najeriya.

Akan haka kocin Super Eagles ya gayyaci matashin ya kalli wasan sada zumunci tsakanin Najeriya da Argentina a Abuja a ranar daya ga watan Yuni.

Sam, wanda ke bugawa Bayer Levekusen kwallo a gasar Bundesliga, mahaifiyarshi 'yar Jamus ce amma mahaifinshi dan Najeriya ne.

Tunda dai bai bugawa babbar tawagar Jamus ba, Sam zai iya koma bugawa Najeriya idan har Fifa ta amince da batun sauya kasarshi.

Siasia yace"na gana dashi a Jamus kuma ya nuna cewar ya san abinda ya dace dashi".

Dan shekaru ashirin da ukun na son ya bugawa Jamus kafin haduwarshi da Siasia a makon daya gabata.

Kocin Najeriya din na saran idan har aka gayyace dan kwallon tabbas zai amsa gayyatar.