Uefa ta yi watsi da korafe-korafen Barca da Madrid

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Irin hayaniyar da ta barke a lokacin wasan Madrid da Barca

Hukumar kula da kwallon kafa ta Turai UEFA, ta yi watsi da koken da kungiyoyin Real Madrid da Barcelona suka shigar biyo bayan karawar da suka yi a gasar zakarun Turai.

Uefa ta ce babu wata shaida ta tunzurawa bayan da Real ta yi korafin cewa Barcelona ce ke da alhakin rashin da'ar da ya faru a wasan.

An dai amince da matakin da alkalin wasa ya dauka na korar Pepe sai dai an yi watsi da korafin da aka gabatar a kan Jose Mourinho.

Sai dai Uefa za ta binciki zargin aikata laifukan da take yi wa kungiyoyin biyu.

Sanarwar Uefa ta ce: "An nemi Barcelona su koma kan zargin da aka yiwa Mourinho tun farko, wanda kwamitin da'a zai saurara ranar Juma'a, 6 ga watan Mayu.

"Don haka babu wani bincike da za a kaddamar a kan Mourinho dangane da korafin da Barcelona suka yi a kansa".

Ana tuhumar Real Madrid ne kan jan katin da aka baiwa Pepe da kuma Mourinho, da kalaman da Mourinho ya yi bayan an tsahi daga wasan, da kuma dabi'ar da magoya bayansu suka nuna.

Yayin da ita kuma Barcelona ake tuhumarta kan jan katin da aka baiwa mataimakin mai tsaron gidanta Jose Pinto a lokacin da aka tafi hutun rabin