Ba za mu ji tsoron Barca ba - In ji Ferguson

Alex Ferguson
Image caption Alex Ferguson yana da babban kalubale a gabansa

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya gayawa 'yan wasanshi cewa bai kamata su ji tsoron Barcelona ba a wasan karshen da za su buga na gasar cin kofin zakarun Turai.

United ta lallasa Schalke da ci 6-1 a wasanni biyun da suka buga, inda a yanzu za ta hadu da Barcelona wacce ta doke ta a irin wannan mataki a shekara ta 2009 a filin wasa na Wembley.

"Ba na zaton za mu fita wasan ba tare da kwarin gwiwa ba," a cewar Ferguson.

"Za mu kara ne da kwararrun 'yan wasa amma hakan ba zai sa gabanmu ya fadi ba. A fili take cewa yanzu lokacinsu ne. Aikinmu shi ne mu san yadda za mu kwaci kanmu." Barcelona ta doke Real Madrid 3-1 a kan hanyarta ta zuwa wasan karshen.

Sai dai Ferguson ya ce zai tattauna da kocin Real Madrid Jose Mourinho a kokarin da yake yi na nemo hanyar yin galaba a kan Barcelona domin rama kashin da suka bashi a 2009.

"Ina yin magana da shi akai-akai," in ji Ferguson. A makon da ya gabata ma na yi magana da shi.