Porto da Braga za su kara a wasan karshe na Europa

Porto da Braga za su kara a wasan karshe na Europa Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasan karshe tsakanin Porto da Brega zai kayatar sosai

Kungiyoyi biyu na kasar Portugal FC Porto da FC Braga za su fafata a wasan karshe na gasar cin kofin Europa a birnin Dublin a ranar 18 ga watan Mayu.

Braga ta doke Benfica da ci daya mai ban haushi inda aka tashi 2-2 bayan wasanni biyu, amma suka tsallake sakamakon kwallon da suka zira a gidan Benfica.

Ita kuwa Porto ta samu kanta ne duk da cewa ta sha kashi a hannun Villarreal da 3-2, sakamakon nasarar da ta samu a wasan farko da ci 5-1.

"Ina ganin mun cancanci zuwa wasan karshe ganin irin rawar da muka taka," a cewar kocin Braga Domingos Paciencia. "Mun nuna cewa karfinmu ya kai kuma za mu sake nuna hakan a wasan karshe."